Labaran duniya
Ƙungiyar Mawaƙan Arewa ta kai wa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ziyara a gidansa da ke Daura
Ƙungiyar Mawaƙan Arewa ta kai wa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.
A makon da ya gabata ne ƙungiyar ta nesanta kanta daga kalaman mawaƙi Dauda Rarara, wanda ya zargi Buhari da lalata lamuran ƙasar.
Kungiyar Mawakan Hausa Mai Suna MURYA ƊAYA, Takai Ziyarar sada zumunci Ga mai girma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a Gidansa dake Daura jihar Katsina.
A ziyarar Tasu Sun Bayyana Cewa basa Tare Da dukkanin Maganganun da Mawaki Dauda Kahutu Rarara Yayi a yan kwanakin nan da Yake nuna Gwamnatin Shugaba Buhari ne Ta dagula Najeriya.
Kungiyar ta haɗa Mawaka irin su Ali Jita, Ado Gwanja, Nazifi Asnanic, Adamu Hassan Nagudu da sauran Su
KBC Hausa News