Labaran duniya

Abba Gida-gida ya Dauki Nauyin Karatun Dalilin 557 zuwa indiya da Uganda

Masha Allah Ganin Sha’awa Kalli yadda Gwamnan jihar Kano Abba Gida-gida ya Dauki Nauyin Karatun Dalilin 557 zuwa indiya da Uganda kuma ya Raba musu dubu N200,000 kamar yadda zaku ganin a cikin wannan bidiyo.

GADAI BIDIYON 👇 

Ɗaliban Kano Sun shiga Jirgi Domin Tafiya Ƙasar Indiya Karatu

Yanzu haka dalibai guda 150 sun shiga Jirgin Air Peace domin tafiya karatu ƙasar Indiya wadda gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin karatun nasu. Ɗaliban zasu tashi a filin jirgin Malam Aminu Kano.

Acikin wannan fili an samu rakiyar ɗaliban ga manya-manyan gwamanti ciki harda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, injiniya Rabi’u Kwankwaso,Dr Abdullahi Baffa Bichi, da sauran su ka yadda zaku BIDIYON kai tsaye.

GADAI BIDIYON ANAN 👇

Ɗaliban sun nuna farin cikinsu bisa wannan abin alkairi da aka yi musu, inda ɗaya bayan ɗaya idan suka zo hawa jirgi suna durƙusar dakai tare da yin Gaisuwa da godiya ga gwamnan Kano. Ɗaliban sun tafi ƙaro karatun ne a fannonin ilimi daban-daban.

Ɗaliban sun samu rakiyar ƴan uwan da abokan arzuƙa, inda wadu ma iyayen su mata da maza sun halarci wannan Filin jirgi, tare da yin farin ciki da kuma yin bankwana da ƴaƴan nasu.

Allah ya sauke su lafiya, Allah ya albarkaci wannan karatu da suka je yi.

Ana sa ran na mintuna kaɗan jirgin zai tashi, da zarar ɗaliban sun kama dai-daita a kan kujerun jirgin, kana suyi Gaisuwa ƙarshe ga gwamnan Kano.

✍️Sulaiman Kabiru Isah

Allah ya saka masa da Alkhairi

KALLI BIDIYON ANAN 👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN