Labaran duniya

Abin Mamaki Baya Karewa! Kalli yadda Wani Matashi Ya Auri Kanwarsa

Munyi karo da wani labari na wata mata ta yi matukar mamaki a ranar auren danta, yayin da ta gano cewa ashe amaryar ’yarta ce wacce ta bace tun shekara 20 baya.

Hakan ya sa mahaifiyar amaryar wacce a rashin sani ta kusa ta zamar mata surika suka fara zubar da hawaye, ita da amaryar da angon, tun bayan da suka gano cewa ita ce ’yarta wacce ta bace da dadewa kuma yanzu take auren danta.

An dai gudanar da wannan bikin ne a garin Suzhou, da ke lardin Jiangsu na kasar China a ranar 31 ga watan Maris.

Sabuwar surikar ta gano ’yar tata ce a lokacin da ake cikin tsakiyar biki, inda ta tabbatar da ’yarta ce ta hanyar gano irin hannunta, kamar yadda kafar yada labarai ta Times Now News ta ruwaito.

Ita dai wannan matar ta fuskanci wadanda suke ikirarin su ne iyayen amaryar, sannan ta tambaye su ko su ne masu rainon amaryar, sai ’yan uwan amaryar suka yi mamakin tambayar da mahaifiyar ke yi masu, duk da yake labari ne mai tsawo.

Daga nan sai suka fara bayyana abin da ya faru da amaryar tun tana jaririya kamar haka: “Wadanda suka raini amaryar sun ce, sun tsinci jaririya a gefan hanya, sai suka dauke ta suna rainonta har ta girma. Kuma sun raine ta kamar ’yar da suka haifa.”

Ita dai wannan batacciyar yarinya ta bayyana yadda ta yi murnar haduwarta da mahaifiyarta fiye da murnar ranar bikinta.

Bayan ta gano abin da ya faru, sai ta nuna damuwarta game da auren, duk da yake shi ma angon dan riqo ne, inda ta karkata ga dan uwan nata.

Angon ya bayyana aniyarsa na auren matarsa kuma ya ce, ba wani dalili na sauya kudirinsa.

A bangaren mahaifiyar, ta ce ba wata matsala a auren tun da ba ’yan uwa ba ne na jini domin kuwa shi ma angon dan riko ne da aka dauko tun yana karami.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN