Labaran duniya

Abinda Tsohon Sarkin Kano Sunusi Khalifan Tijjaniya Na Kasa Yayi Ya Jawo Masa Magana

Ko Ya Dace Khalifa Sunusi Ya Dinga Shan Hannu Da Mata?

Daga Indabawa Aliyu Imam

Batun gaisuwar shan-hannu da Maimartaba Khalifa Muhammadu Sunusi Na Biyu ke yi da Matan da ba Muharramansa ba ba daidai ba ne. Ba maganar hassada ba ce. Domin duk adawar mutum da Maimartaba Khalifa ya san Khalifa mutumin kirki ne wanda Allah ya yi wa tarin baiwa da daukaka da ‘yan kalilan na mutane ne kadai ke samun ta.

Maimartaba Khalifa Malamin addinin musulunci ne wanda yake da dumbin ilmin addini kuma uwa uba Allah ya hore masa haddar Alqur’ani da harshen larabci. Bangaren Boko kuwa, ba ma za a ce komai ba domin masu abu ne da abinsu.

Daukakar da Allah ya ba wa Khalifa ta zarce Najeriya ko Afirka, magana ake ta manyan kasashen duniya irinsu Amurka da Burtaniya na gayyatar sa taron majalisar dinkin duniya don neman gudummawarsa. Lallai wannan kadai abu jin dadi da alfahari ne ga kasar Najeriya musamman ma jiharmu ta Kano wanda ni ma dan cikinta ne.

Ya kamata Maimartaba ya san cewa a yanzu shi Dattijo ne, kuma Jagoran Dariqar musulunci ta Tijjaniya wanda ya zamanto tamkar wani Madubi ga al’ummarsa ya kuma zamanto wata fitila da ke haskake al’umma suke samun fa’ida daga wannan haske. Khalifa yanzu abun kwaikwayo ne, don haka a dinga sara ana duban bakin gatari, duk da kasancewar kowa na yin kuskure d’an adam ajizi ne kuma mutum tara yake bai cika goma ba. Amma kuskure irin wannan a bainar jama’a, ga babban mutum irin Khalifa, wani babban kalubale da aibu ne a gare shi da mabiyansa. Don Allah makusantansa ku ankarar da shi. Ta’ba hannun mace kuskure ne saboda Annabi SAW ya hana.

Baihaki da Tabarani suka fitar da shi. Manzon Allah S.A.W ya ce”

لأن يطعن في رأس أحدكم بمخيط من حديد خير له من أن يمس امرأة لا تحل له.

“Gwara a soki kan mutum da allurar karfe da ya ta’ba macen da ba ta halatta gare shi ba”.

Bukhari ya rawaito Nana Aisha A.S ta ce”
والله ما مست يده يد امرأة قط في المبايعة،
“Wallahi hannun Annabi S bai taba shafar hannun wata mace ba a yayin mubayi’a.

Ta sake cewa a wani kaulin”

وما مست يد رسول الله صلى الله عليه و سلم يد امرأة إلا امرأة يملكها
“Hannun Annabi bai taba shafar hannun wata mace ba, sai wacce yake mallakarta”

Nasa’i ya fitar(4181) da Musnad na Imamu Ahmad (2874) wanda Albani ya inganta shi, sanda mata suka yi nufin yi wa Annabi mubayi’a sai ya ce musu,”

إِنِّي لَا أُصَافِحُ النِّسَاءَ، إِنَّمَا قَوْلِي لِمِائَةِ امْرَأَةٍ كَقَوْلِي لِامْرَأَةٍ وَاحِدَةٍ
“Hakika ni ba na gaisawa da mata, maganata ga mata dari kamar ga mace daya ce.”

“Tunatarwa ce, domin tunatarwa na amfanar da mu’uminai.” وذكر فإن الذكرى تنفع المؤمنين

Ban son tsawaitawa, a matsayina na dalibi, wadannan hujjoji ne dake kalubalantar masu cewa yin hannu da mace daidai ne. Ko da a ce Khalifa na ganin hakan daidai ne, sai ya dinga yin abunsa a boye ba tare da hoto an bayyana wa duniya ba.

An ba ni labari cewa sanda Maimartaba Khalifa yake matashi mutum ne mai tsaurin ra’ayin addini, da shi ma aka yi batun Gidiwe. Amma daga baya sai ya sassauta ra’ayinsa har sassautawar ta zarce iyaka, wanda shi ne mafarin adawarmu da shi. Bayan cire shi daga Sarauta da gwamnatin Kano ta yi, an sami sauye-sauyen masu yawa daga ra’ayoyinsa, wato “Afkar da Mu’utaqadaat dinsa” ya dawo da bin nassosi da hukunce-hukuncen shari’a wanda muka yi matukar farin ciki.

Duk da wannan kuskure muddin za mu yi adalci tabbas Khalifa mutumin kirki ne mai dumbin alkhairi wanda daukakarsa ba ta hana shi tawadhu’u da kaskantar da kai ba, don ni na gani a aikace. Hakika tarihi ba zai mance alkhairan Khalifa ba wanda ya yi uwa ya yi makarbiya aka samar da Bankunan musulunci Jaiz da Taj. Bayan zamowarsa Sarkin Kano ya kasance wani bango na talakawa da marasa galihu yadda yake raba musu abinci da siya wa marasa lafiya magani. Sanda Boko Haram suka farmaki masallacin Masarauta, Khalifa ya dauki nauyin da yawan wadanda suka jikkata, ya kuma rage wa iyalan wadanda suka rasu radadi. Hallau dai Khalifa ya zamo Sarki mafi adalci a jihar Kano ta yadda yake kwato wa masu rauni hakkinsu daga wajen azzalumai, ya sha hukunta Hakimai da dagatan da suka yi zalunci, bayan dumbin alkhairai da yake yi wa ma’aikatan Masarautar Kano. Khalifa ya yi amfani da sarautarsa ya’ki shi’anci da zagin sahabbai a Kano da wani d’an iskan mutum ke yi a Gwale filin mushe. Ko a wancan lokacin mun goyi bayan matakin da Khalifa ke d’auka kan azzaluman mazan da ke azabtar da matayensu suna dukan su suna barin su ba ci ba sha. Da yawanmu wadanda ke adawa da shi suna kalubalantar matakinsa na takaita iyalai ga wanda ba shi da iko, amma ni Indabawa Aliyu Imam ina tare da shi a nan. Mutum ne za ka ga albashinsa bai wuce 20k ba amma ya auri mata uku kowacce da ‘ya’ya ya bar su su yi ta gararamba a gari ba ci ba sha, addini ma bai amince da haka ba.

Allah ya taimaki Khalifa ya ba shi ikon gyarawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN