Labaran Kannywood

ABINDA YASA NA FARA Rawa DA WAƘA A GIDAN GALA – TAHIR FAGGE

ABINDA YASA NA FARA Rawa DA WAƘA A GIDAN GALA – TAHIR FAGGE

DAGA Hauwa Farouk Ibrahim

“Lokacin da abin ya faru, ina kwance ne a gida, ba ni da lafiya; na samu matsalar cutar shanyewar ɓarin jiki, har ya zama ba zan iya tafiya mai tsayi ba a lokacin har sai na zauna na huta. Kuma ba ni da kuɗin da zan je asibiti, kuma ina neman kuɗi N260,000 wanda da shi ne za a ɗauki hoton zuciya ta, za a ɗauki hoton ƙirji na da yi mani magani.

“Yaran nan su ka zo har gida su ka same ni, su ka ce ko da ba zan yi rawa ba, su na so na je wajen na zauna a matsayi na na babban baƙo. Kuma a nan su ka ɗauki kuɗi N160,000 su ka ba ni. Ka ga saura N100,000 kenan.

“A lokacin na ga duk wanda ya faɗa ruwa idan aka ba shi takobi zai kama, don ya na neman ceto. Da na je wajen na zauna sai masoya su ka roƙe ni da na tashi ko tsayawa na yi a kan fulo, su ka samo tsohuwar waƙar da na hau tun a finafinan baya su ka saka. Sai aka riƙa yi mani liƙi, wanda kuma alhamdu lillahi a wannan lokacin na samu cikon N100,000 ɗin da na ke nema da zan haɗa a yi mani aikin, har ma da wasu kuɗin da na riƙe a hannu ina ci da iyali na lokacin da na ke zuwa asibitin.

“Amma su da su ke maganar, me su ka yi mani don ceto rayuwa ta?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN