Labaran duniya

Abu Kaɗan Sai A Riƙa Cewa Anya Ni Musulma Ce? In Daina Sa Hijabi, Munafukan Banzà Munafukan Wofí, Cewar Aisha Yesufu

Abu Kaɗan Sai A Riƙa Cewa Anya Ni Musulma Ce? In Daina Sa Hijabi, Munafukan Banzà Munafukan Wofí, Cewar Aisha Yesufu

Shararriyar ƴar gwagwarmayar nan Aisha Yesufu, ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook wanda ya jawo cece-kuce, yayin da ta bayyana yadda mutane ke hantarar ta tare da bayyana ta a matsayin wacce ba musulma ba.

Yesufu dai tayi rubutun nata cikin ɓaci rai inda ta bayyan cewar har ta kai mutanen na cewa ta daina sa Hijabi.

“Abu kaɗan anya musulmace? Ba musulma ba ce ba, ki daina sa hijabi.”

“Munafukan banzà munafukan wofí, a ga musuluncin ku a ƙasa. Banda talauci, da yaudara, da danne haƙƙin yara da mata me kuka sa gaba? Ina abun kwadanta ma mutane musulunci? Kashe kashen? Fyaɗen? Zubar da yara a titi? Ƴan mata masu talla? Cin amanar? Rashin kula da marayu? Aikin ɓar in ji tusa, a nuna mana zahiri a ƙasa.” Inji Yesufu

Ya zuwa yanzu dai mutane sama da dubu biyu ne suka tofa albarkacin bakinsu akan wannan wallafar rubutu na ta, inda wasu ke ƙara caccakarta, wasu kuma ke bayyana hakan da ake yi mata bai dace ba.

Me za kuce?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN