Abun ayaba Jaruma Sayyada A’isha Humaira A Yau Ta Kai Tallafin Gudummawar Kayayyaki Gidan Yarin Kurmawa
Jaruma Sayyada A’isha Humaira A Yau Ta Kai Tallafin Gudummawar Kayayyaki Gidan Yarin Kurmawa
Kamar yadda ta saba kai gudunmawa gidan gyaran hali da tarbiyya a lokuta daban-daban, a yau ma fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, A’isha Humaira ta kai ƙarin tallafin kayayyakin amfanin yau da kullum gidan gyaran hali da tarbiyya na Jihar Kano (Kurmawa).
Kayayyakin da ta kai sun haɗa da: bokitai dozin 12 wanda ya kama guda 150, da Magin cin abinci da girki katan 10, da omon wanki katan 10, da gidan sauro guda 50, da butar alwala dozin 12, da katifu guda 20, sai kuma tabarma rol 2 wadda ta kama guda 50 a jimlace.
Humaira ta shahara kan ayyukan jinƙai da taimakon al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi da marayu. Ta sha biya wa ɗaurarru masu ƙananan laifuffuka tarar kuɗaɗen da aka sa musu domin su shaƙi iskar ƴanci. Haka zalika, ba wannan ne karon farko da ta ke kai gudunmawar kayayyakin amfanin yau da kullum gidajen gyaran hali na faɗin jihar ta Kanon ba.
Mutanen da suke amfana da tallafin da hatta su kansu ma’aikatan gidajen gyaran halin suna yaba wa da jinjina mata kan wannan ƙoƙari da ta ke yi.