Labarai
Alhaji Obobo Ya Sake Ɓaro Aiki Ya Ɗaura Niyya Zuwa Dubai A Keke
Alhaji Obobo Ya Sake Ɓaro Aiki Ya Ɗaura Niyya Zuwa Dubai A Keke
Haziƙin matashin nan, kana gwarzo da ya je Makka a keke yanzu haka ya ɗaura aniyar zuwa ƙasar Dubai akan keke a shekarar 2025 wato shekara mai zuwa.
Alhaji Ali Obobo wanda ya ƙi sayar da kekensa Naira miliyan 40 a Makka bayan da wani Balaraben ƙasar Egypt ya buƙaci a sayar masa da keken, amma yayi ƙememe saboda kishin Najeriya, ya kyautar da keken a gidan tarihi a Legas daga nan ne kuma yayi tattaki a ƙasa zuwa Maiduguri.
Yanzu haka ya ɗaura aniyar tattaki zuwa jihohi 6 bayan azumi, sannan kuma ya shaida wa majiyar mu cewa a shekarar 2025 zai tafi Dubai a kan keke da yardar Allah.