Labaran Kannywood

Allah sarki Kalli Bidiyon Yadda akayi Jana’izar Marigayi Kamal Aboki yan Kannywood sun fashe da Kuka

Kamal daya ne daga cikin mutanen da suka daukeni tamkar ciki daya muke, yana karbar shawarata yakan kirani ya gaidaki, yazo inda nake, babban abinda yake burgeni dashi girmama mutane da fara’a…

Bazan manta wannan ranar ba, Kamal Aboki yace dani oga bari nayi maka hoto, zan ajiye tarihin nayi tafiya da kai zuwa Maiduguri, muna wasa da dariya nace kajika da zolaya sai kace kayi tafiya da wannan babban mutum, cikin hukuncin Allah ashe hoton ne zai zama tarihin ka a gurina, Allah yayi maka Rahma Kamal, domin Kamal ba dan barkwanci bane kawai, mutum ne mai hankali nutsuwa da girmama mutane, Allah ya sani bansan wani aibun Kamal da zan iya fada a duniya ba, wannan tasa dole muji zafin mutuwarsa, amma duk son da muke masa Allah yana masa wanda yafi namu, shi yasa ya kirashi zuwa gare shi.

Allah ya gafarta masa yasa aljanna makomarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN