Allah sarki kalli Bidiyon Yadda akayi Jana’izar Marigayi Umar Yahaya Malunfashi
Allah sarki kalli Bidiyon Yadda akayi Jana’izar Marigayi Umar Yahaya Malunfashi, Yan Kannywood na jimamin rasuwar Kafi Gwamna
Yan fim da furodusoshi da daraktoci da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun yi ta bayyana jimami da alhinin rasuwar fitaccen dan wasan nan Umar Yahaya Malumfashi da aka fi sani da Bankaura ko Kafi Gwamna. A daren Talata 27 ga watan Satumba ne, Allah ya yi wa fitaccen jarumin rasuwa a wani asibiti da birnin Kano a arewacin Najeriya, bayan fama da rashin lafiya.
Umar Malumfashi wanda akafi sani da suna Bankaura a cikin tsofaffin finan-finan Mausa tun kafin kafa masana’antar Kannywood, yayin da a wannan zamanin kuma ake kiransa da sunan Yakubu ka fi gwamna, saboda rawar da ya ke takawa a shirin Arewa24 mai dogon zango wato Kwana Casa’in.
Bankaura ya taka muhimmiyar rawa domin ciyar da masana’antar Kannywood gaba, yana daya daga cikin yan wasan dade a masana’antar.Ya yi zamani da manyan iyaye mata da maza a masana’antar, irin su marigayiya Hajiya Amina Garba
(Hajiya Dumba, ko Hajiyar falo), da marigayiya Hawwa Ali Dodo (Biba) da marigayiya Jamila Haruna, da su Hajara
Usman, Saratu Gidado (daso) da sauran su.
Zakuji cikakken a cikin Bidiyo kasa: