Kannywood

Allah Sarki Rayuwa 😭 Kalli Silar da tayi Mutuwar Manyan Jaruman Kannywood a wannan Shekarar

Allah Sarki Rayuwa 😭 Kalli Silar da tayi Mutuwar Manyan Jaruman Kannywood a wannan Shekarar

SARATU GIDADO ( DASO )

Yan uwan ​​jarumar da suka zanta da gidan rediyon Freedom ne suka tabbatar da wannan labarin mai ban tsoro, inda suka bayyana cewa an samu Rasuwar Daso a safiyar ranar Talata.

A cewar ’yan uwan da Margayiya, an gano cewa Daso ta rasu ne bayan ta koma ta kwanta bayan ta yi Sahur, abincin da ake ci kafin a yi azumin watan Ramadan.

Rasuwarta ba zato ba tsammani ya bar masana’antar da magoya bayanta cikin tsananin bakin ciki.

FATIMA SAID ( BINTU DADIN KOWA )

Fatima Sa’id, wacce aka sanar da rasuwarta a ranar 11 ga Fabrairu, 2024, ta kasance shahararriyar jarumar Kannywood wadda ta fito a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa24. An haifi Bintu Dadin Kowa a shekarar 1999 kuma ta fito ne daga Gunduwawa, karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, Neptune Prime ta ruwaito. Ta fara wasan kwaikwayo ne bayan ta fito a wani fim mai suna “BIL HAKKI”, daga baya kuma tauraruwarta ta fara haskawa bayan ta fito a shirin “Dadin Kowa”.

KAWU MALA ( AMINU MUHAMMAD)

A yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Mayun 2023 Allah ya dauki rayuwar Malam Aminu Muhammad wanda aka fi sani da Kawu Mala a shirin ‘Dadin Kowa’ na tashar Arewa24. Rahoton jaridar Aminiya ya bayyana cewa ciwon zuciya ne ya yi silar ajalin jarumin, wanda ya bar mata daya da yara 12. Kannywood ta kadu da rasuwar Kawu Mala saboda dattakonsa.

AMINU S BONO

Ba a gama jimamin rasuwar Samanja Mazan Fama ba, Kannywood ta sake girgiza da rasuwar babban darakta kuma jarumi, Aminu S. Bono, wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2023. Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha ne ya sanar da rasuwar Aminu S. Bono a shafinsa na Facebook, mutuwar da aka juma ba a ji irin ta a masa’antar ba.

HANNATU UMAR

Jaruma Hannatu Umar ta amsa kiran mahalicci a gidan yayarta da ke unguwar Katampe a Birnin Tarayya, Abuja, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito.

Wani abin tava zuciya da mutuwar jarumar shi ne, ba ta tare da wata rashin lafiya bare har a yi mata zaton mutuwa, domin wani makusancinta ya tabbatar da lafiya ƙalau ta tashi daga barci, har ta yi shiri don fitowa falo da zummar yin kalaci, akan hanyar isa falon ne ta yanke jiki ta faɗi, wanda hakan ya zama sanadin tafiyar ta.

NURA MUSTAPHA WAYE 

AN wayi gari a yau da bakin labarinrasuwar Malam Nura MustaphaWaye, daraktan fitaccen shirin nanmai dogon zango mai suna lzzarSo’.

Nura ya rasu ne a safiyar yauLahadi, 3 ga Yuli, 2022, da misalinkarfe 8:00 na safe a wani asibitiaKano.

An yi jana’izar sa da misalin karfe11:00 na safe a gidan sa da keunguwar Goron Dutse, Kano.

Yan fim da mutanen gari sunhalarci jana’izar, inda wurin ya cikamakil babu masaka tsinke.

ZAKUGA CIKAKKEN JARUMAN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA TA HANYAN KALLON BIDIYON DAKE KASA

GADAI BIDIYON 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN