Allah Sarki Rayuwa, Kalli Ýaya da Dukiyar da Margayi Rabilu Musa Ibro ya Bari, Muna Fatan Allah ya Jikanshi da Rahama
Cikaken Tarihin Ibro
Rabilu Musa Ibro, Anfi sanin sa da suna Dan Ibro (Disamba 12, 1971 – Disamba 9, 2014) kwararren dan wasan barkwanci ne na Hausa a Najeriya mai shiryawa jarumi kuma mai bayar da umarni na fina finan Hausa. Ana kallonsa a matsayin jagoran cigaban masana’antar fina finan Hausa na Kannywood, ya ciyar da masana’antar gaba sosai har zuwa rasuwar sa a shekarar 2014.
- Haihuwa: An haifasi a Wudil, 12 Disamba 1971
- Mazauni: Kano
- Mutuwa: Kano, 9 Disamba 2014
- Sana’a: ɗan wasa
Dan Ibro ya halarci makarantar Danlasan Primary School, a garin Wudil daga baya ya je makarantar Government Teachers College Wudil duka a jahar Kano. Ya shiga aikin jami’in tsaro na gidan yari wato Nigerian Prison Service a 1991 yayi kuma aiyukan sakai. Daga baya kuma duka ya koma harkar fim da fim dinsa na farko wato Ƴar mai Ganye wanda ya kara bunkasa harkokin sa.
Shahararrun wakokin da suka kara bunkasa shu sune Bayanin Naira, Idi Wanzami, Dureba Makaho.
Rabilu Musa ya shahara sosai a harkar fina finan hausa kadan daga fina finan sa sun hada da Andamali, Bita Zai Zai, Ibro Aloko, Ibro Angon Hajiya, Ibro Dan Fulani, wasu wakoki daya shahara dasu sune Bayanin Naira, Idi Wanzami, Direba Makaho.
Allah ya jikanshi da rahama.
Babban da ga shahararren jarumin fina finan Hausa Rabilu Musa Ibro, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekaru 9 da suka gabata, Hanafi Rabilu Musa Ibro ya bayyana yadda har yanzu suke amfanuwa da zaman arziki da mahaifinsu ya yi da mutane a lokacin da yake raye.
Inda ya kara da cewar iyalan marigayi Ibro suna matukar jin dadi idan suka ji ana yi wa mamacin addu’ar samun rahamar Ubangiji.A kowane lokaci mu kan ji ko kuma a fada mana cewar mahaifinmu ya samu kyakkyawan yabo a wajen mutanen da ya yi mu’amala dasu da kuma wadanda yake sakawa nishadi.
Kadan daga Cikin yaran marigayi Rabilu Musa ibro
Hannafi Ibro
Maryam Ibro
Jawahir Ibro
Ahmad ibro
Sadiq Ibro
Feisal Ibro
Jafar Ibro