Allah sarki rayuwar duniya kenan bidiyon murjih Ibrahim kunya a gidan yari yanzu..
Allah sarki rayuwar duniya kenan bidiyon murjih Ibrahim kunya a gidan yari yanzu..
AN SAKE TASA KEYAR MURJA DA SAURAN ABOKAN TA ZUWA GIDAN YARI
Daga Shuaibu Abdullahi
Wata Kotu a Kano ta sake tura jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya gida yari, bayan sake zaman ci gaba da shari’ar da ake yi da ita yau Alhamis.
Haka zalika kotun ta kuma aike da abokin Murja, Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya da Sadiq wanda ya yii wakar “A daidai ta nan” da kuma Aminu BBC zuwa gidan gyaran halin.
Gadai Bidiyon
Kafin yanzu zauren malaman Kano ne ya gurfanar da Murja a gaban Kotun kan wasu dabi’un rashin da’a, wanda aka daga zaman zuwa yau 16 ga watan.
Har ila yau yayin zaman na yau zauren Malaman ya sake gurfanar da wasu matasan gaban kotu, bisa zarginsu da wallafa kalaman batsa a dandalin TikTok, da waka.
Bayan zaman na yau Alkalin kotun ya tura su gidan yari har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu don cigaba da sauraren shari’ar.
DIMOKURADIYYA