Labaran duniya

Allah Sarki Saurari Wasiyar da Malam ya Bari Kafun Rasuwarsa 😭😭😭

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭  Allah Sarki Saurari Wasiyar da Margayi Malam Giro Argungu ya Bari kafun Allah ya Dauki Rayuwarsa.

KALLI WANNAN BIDIYON 

A Jiyane dai Allah ya Dauki rayuwar Margayi Sheikh Giro Argungu wanda ayau za ayi Jana’izarsa kamar yadda magabata suka sanar, Malam yana daya daga Cikin Fitattun Malam Izala wanda suka bada gudunmawa dukkan fadin Nijeriya.

Kafun Rasuwar Malam Sai da Yaja Kunnen Dukkan Muslumai Inda yabar Wasiya Kafun Allah ya Karbi Rayuwar.

GADAI WASIYAR DA YA BARI A WANNAN BIDIYON:

PLAY

SHEIKH ABUBAKAR GERO
Rahimahullah YACE

In kun sami labarin mutuwar mu kuyi mana Addu’a, ku roki Allah ya karbi ayyukan mu, bamu da matsala a duniya da ta wuce qaqa zamu mutu, na biyu Allah ya karba bai karba ba wallahi wallahi bamu sani ba, amma yana yuwa addu’oin ku su taimaka Allah ya yaye zunuban mu ya karbi ayyukan mu, wallahu a’alam.

SHEIKH ABUBAKAR GIRO ARGUNGU.

Yace: ❝Ka ƙirgawa kanka duk garin ku shekara nawa ag-ga mutanen garinku. nawa ya rage maka. ko ba mutuwa ba, tsufa yana zuwa, tun kuna iya gudu, za ku cimma sanda baku iya gudu. tun kana cin abu mai daɗi, za ka cimma lokacin da baka iya cin mai daɗi, Allahu Akbar❞

“Da yawanmu mukan ɗauki rayuwar duniya tamkar wata madauwama, mukan rayu cikin duniya yadda kasan baza mu mutu mu barta ba, rayuwar duniya ta rufe mana idanu bama hangen ta lahira sai ƴan kaɗan daga cikinmu”

“Ka dubi dubban al’ummar da suka shuɗe gabanin ka, kallon haka kaɗai ya isheka wa’azi idan kana da rabon wa’azantuwa, da yawa sun mutu sun barmu, wanda kuma hakan shi ne yake nuna mana cewa tabbas watarana muma za mu mutu mu bar wannan duniyar wallahi”

“Bijirewarka da yawan saɓon Allahnka ba shi ne zai hana ka riski wannan ranar ta rabuwarka da duniya ba. Haka nan nagartarka da jin tsoron Allahnka, ba shi ne zai hana ka mutuwa ba, duk yadda ka kasance wallahi sai mutuwa ta ɗauke ka, sabida haka yafi maka adalci ga kanka ka nutsu kaiwa Allah ta’ala biyayya”

Allah ta’ala kaji ƙan mamatanmu, ka kyautata makwancinsu, muma kasa mu mutu kana mai yarda damu baki ɗaya.

Muhammad Umar Baballe
Abu Amatillah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN