Allah Sarki Yanzu-Yanzu Bazoum yayi Magana tun Bayan da akayi Masa Juyin Muki
Allah Sarki Yanzu-Yanzu Bazoum yayi Magana tun Bayan da akayi Masa Juyin Muki
A jiya ne dai Akayiwa Shugaban kasar Niger Muhammadu Bazoum juyin wanda inda aka saka shi da karfi Ya Saka Hannu a takardar mika Mulki ga Soji, sai dai tunda wannan lamarin ya faru baji ta bakin Bazoum ba.
Wanda a yanzu shine karon farko da Yayi Bayani ga dai Bidiyon a kasa:
PLAY ▶️
Hambararen shugaban Nijar Mohamed Bazoum a karon farko tun bayan kifar da gwamnatinsa da sojoji suka yi a jiya Laraba, ya bukaci al’ummar kasar da su kwantar da hankalinsu, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Kazalika Bazoum a ce za a kare duk wasu nasarorin Nijar, kuma ‘yan kasa da ke kishin dimukradiyya da yanci za su tabbatar da hakan.
Ina fatanku ga Shugaba Bazoum?
A Gaggauta Sakin Bazoum Ba Tare Da Bata Lokaci Ba, Cewar Majalisar Ɗinkin Duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojojin da suka hambarar da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, kuma suke tsare da shi da su gaggauta sakin shi.
Jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasar ne, suka tsare Bazoum a Yamai a ranar Laraba, wadanda bayan sa’o’i kadan suka sanar da karbe mulkin kasar.
“Na yi matukar kaduwa da damuwa game da yunkurin da sojoji suka yi a Nijar kuma na yi Allah-wadai da lamarin. Dole ne a yi duk mai yiwuwa don dawo da tsarin tsarin mulki da bin doka da oda,” in ji babban jami’in kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk a wata sanarwa ranar Alhamis.
Ya kara da cewa, “Dole ne a gaggauta sakin Shugaba Mohamed Bazoum ba tare da wani sharadi ba, kuma a tabbatar da tsaronsa. Su ma mambobin gwamnatinsa da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba dole ne a sake su ba tare da wani sharadi ba.
“Ina kira ga duk wadanda ke da hannu da su guji tashin hankali da mutunta hakki da ‘yancin kowa. Yana da kyau a da kiyaye muhimman nasarorin da dimokuradiyya ta samar a ‘yan shekarun nan ga al’ummar Nijar.”
Nijar ta bi sahun kasashen Yammacin Afrika irin su Mali da Burkina Faso da suka fuskanci juyin mulki a baya-bayan nan.