Labaran duniya
Allah yayiwa Dareta Ashiru Nagoma rasuwa
Tabbas daga Allah muke kuma gare shi zamu koma,Allah yayiwa fitaccen Daraktan nan kuma jarumi a finafinan 2000 Ashiru Nagoma rasuwa.
Daraktan ya kasance fasihi kuma
fitacce a lokacin sa,kafin daga bisani ya samu matsala wadda ake alakanta ta da asiri ko kuma muce sammu.
A shekaru 2 baya da suka wuce an
tabbatar da cewa yana fama da matsalar kwakwalwa wanda daga bisani aka nema mishi magani,daga karshe aka dena jin duriyar maganar.