Labaran duniya

An gano Cewar An Sakawa Asiwaju Tinubu Na’urar Da ke Tattara Fitsari A Jikinsa

AKwai Yuwuwar An Sakawa Asiwaju Tinubu Na’urar Da ke Tattara Fitsari A Jikinsa.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Wani sabon hoton Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana, inda ya sanya wata na’urar ciki da ake kyautata zaton ‘bukan catheter’ ne don fitar da fitsari, lamarin da ke ƙara tayar da hankulan ƴan Najeriya game da rashin lafiyarsa.

Catheter na’ura ce da ke tattara fitsari a cikin jakar magudanar ruwa ta bututun da aka maƙalawa masu yoyon fitsari. Yawanci mutanen da ba za su iya fitar da fitsari a zahiri ba suke amfani da shi.

Wani mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Joe Igbokwe, ne ya fitar da hoton a ranar Alhamis da rana, a wani yunƙuri na kawar da damuwa kan tafiyar da ya yi a Landan, ciki har da rashin halartar yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi yau a Abuja.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour (LP) ne suka halarci taron, inda Mista Tinubu ya samu wakilcin abokin takararsa Kashim Shettima.

Hoton da aka yaɗa a shafukan sada zumunta a matsayin ‘shaidar rayuwa’ ya nuna malam Tinubu ya gana da tsohon shugaban riƙo na jam’iyyar APC, Bisi Akande, da Najatu Muhammadu, wata jigo a jam’iyyar.

Jaridar Gazette ta tattaro cewa ɗan takarar na jam’iyyar APC ya tafi ƙasar Birtaniya ne, a ƙarshen makon da ya gabata, kwanaki kaɗan kafin jam’iyyar APC ta fitar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar mai wakilai 422 (PCC).

Tafiyar na sa na ba zato ta kuma ƙara rura wutar jita-jitar wani balaguron jinya kamar yadda ya yi iƙirarin cewa ya da ce don yaƙin neman zaɓe na zaɓen shekara mai zuwa.

Likitoci huɗu, ciki har da likitocin fiɗa biyu, sun sanar da jaridar The Gazette cewa jigon “jakar fitsari” ya bayyana a hoton Mista Tinubu.

Tun lokacin da ya shiga takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023, ciwon Mista Tinubu ke tada hankali a tsakanin ƴan Najeriya, musamman masu sukar halayen sa, waɗanda ke neman ya dace ya gaji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a shekara mai zuwa.

A watan Fabrairu, jaridar The Gazette ta wallafa wani faifan bidiyo na ziyarar da malam Tinubu ya kai fadar Awujale na Ijebuland da ke Ijebu Ode wanda ya bayyana yadda rigar sa ta jike a bayansa lokacin da ya miƙe don yi wa maziyarta jawabi a fadar.

An kuma hangi ɗaya daga cikin mataimakansa na tsaro ya rufe hancinsa a cikin faifan bidiyo.

Hotunan dai ya janyo suka daga ƴan Najeriya, inda da dama ke cewa hakan na nuni da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na fama da matsalar yoyon fitsari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN