An lakaɗawa maɗagwal dukan tsiya saboda rashin saka hannu ayiwa matarsa aiki
An lakaɗawa maɗagwal dukan tsiya saboda rashin saka hannu ayiwa matarsa aiki.
“Shahararren ɗan wasan barkwancin nan mai suna Ali Artwok, wanda aka fi sani da Maɗagwal, ya sha dukan tashi kasha ruwa a Asibitin Barau Dikko da ke garin Kaduna, sakamakon ƙin sanya hannu a takardar shaidar fiɗa da za’a yi wa matarsa Hawa’u.”
“Matar nasa Hauw’u wadda ta shafe kwanaki uku ta na dogon naƙuda kuma likitoci sun tabbatar ba za ta iya haihuwa da kanta ba, bisani Maɗagwal ya ce shi yasan matarsa zata haihu da kanta in kuma ta mutu to shihada ta yi.
“Mahaifiyar Hauwa’u ta bayyana wa Jaridar Fasihiya baƙin cikinta da faruwar lamarin, domin har zuwa yanzu da Ƴar uwar Hauwa”u ta sa hannu kuma suka biya kuɗin aikin Maɗagwal ya ce bai yi nadama ba, kuma ba zai ƙyale duk wanda ya yanka masa mata ba.
“Anyi nasarar ciro ɗa namiji zuwa yanzu. kuma za mu ci gaba da bibiyar lamarin kamar yadda rahoton hakan ke tabbatar mana da hakan.”