An zargi malamin addinin islama wato Isah Ali Pantami da sanya Cross a jikinsa
An zargi malamin addinin islama a Najeriya da sanya Cross a jikinsa
Wani shafi sada zumunta na facebook mai suna Takiyya izala ya wallafa hoton ministan harkokin sadarwa a Najeriya kuma shahararren malamin addinin Islama Dr lsa Ali Fantami inda ya yi zarqin cewa wai malamin ya sanya wata kwalli a rigar jikinsa mai dauke da alamun Cross.
Gadai Bidiyon
A wani labarin kuma. Yadda Shari’ar Sheikh Zakzaky da ya shigar tsakaninsa da NIA kan rike masa Fasfo ta kaya. Sheikh El-Zakzaky da NIA: An Sake Dage Zaman Kotun Zuwa Wata Febrairu. Bayan tsawon lokaci da aka zauna, a jiya Laraba ma kotun ta sake zama, inda mai shari’ar ya dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Fabarairu shekerar nan. Lauyan Sheikh lbraheem Zakzaky da Matarsa Malama Zeenah, Barrister Abubakar Marshall ya bayyana cewar zasu sake dawowa domin cigaba da zaman kuma suna jin kamshin nasara akan abunda suka sa a gaba. Sai dai a bangare guda kuma Almajiran Malamin ne Mazansu da matan su suka yi dafifi a kofar kotun domin neman a
saki Fasfo din Malamin nasu.
Idan har Mai karatu bai mantaba, tun bayan Shakar iskan yanci da jagoran mabiya Shia yayi tare da Matarsa Malama Zeenatudden daga tsarewar da gwamnan Tarayya tayi masu, Shehin yake son fita kasar waje Domin cigaba da duba lafiyarsa tare dana Matarsa Amma lamarin ya cutura. Inda ake zargin cewa Hukumar DSS tare da hadin kan wasu kungiyoyin gwamanti suka rike Fasfo din Shehin don hanasa ko motsawa daga nan gida Nijeriya zuwa wata kasar Neman Lafiya.
a Sahara Reppters Hausa.