Labaran duniya

Anata raɗe-raɗin cewa Tinubu ya kamu da cutar rawar jiki “Parkinson”- Atiku Abubakar

Anata raɗe-raɗin cewa Tinubu ya kamu da cutar rawar jiki “Parkinson”- Atiku Abubakar

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi izgili da yanayin lafiyar takwaransa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki.”

Da yake zantawa da “TheCable” ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, a ranar Litinin, Atiku ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su ɗauki duk wani dan takarar shugaban ƙasa da yake da lafiya.”

“Tsarin zaben shugaban ƙasa ba jam’iyya ba ce don haka tun da farko APC ta haɗa gidanta da cike da ƙarerayi, Bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba saboda rashin iyawarsu na wurin gudanar da mulki.”

“Atiku Abubakar ya cigaba da cewa Kada wanda ya ya ɗauki ɗan takara da yanayin jam’iyyar suka ruguza ƙasa, kamar shi kuma Ɗan takaran nasu makarantar farko, da shekarunsa duk a ɓoye suke. Babu wanda ya isa ya ɗauki irin wannan ɗan takara da muhimmanci.”

“Atiku har wala yau dai a cikin jawabansa Ku tuna cewa yanayin lafiyar Tinubu ya haifar da damuwa da tambayoyi masu yawa a tsakanin ‘yan Najeriya kuma mutane da yawa sun yi jayayya cewa mai yiwuwa ya kamu da cutar Parkinson, rashin lafiya wanda ke shafar motsi, sau da yawa ciki har da rawar jiki.”

“Wannan shi ne musamman yadda aka lura a lokuta da dama cewa shi (Tinubu) yana da wahalar riƙe abubuwa da kyau.”

Source: ALFIJIR HAUSA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
KALLI BIDIYON ANAN