Labaran duniya
Angon da Ya auri mata Takwas Lokaci Guda, Ya Bayyana yadda Ya Sha dakyar a Daren Farko
Nasha Wahala a darena na farko,
Angon mata takwas reras a rana ɗaya.
Daga Hajiya Mariya Azare.
“Wani matashi dan kasan thailanda ya bayyana yadda yasha wahala a daren shi na farko inda ya auri mata 8 rana ɗaya reras.”
“Angon mai suna Ong Dam Sorot, dan ƙasan thailand mabiyin addinin hindu mai sana’an zanen tattoo, ya bayyana yadda daren shi na farko ya bashi wahala inda kowacce tace itace ta farko a gidan.
Ong yace da taimakon abokinsa aka shawo kan wadannan matan inda yabi kowace ɗaki a rana ɗaya yayi kwanciyar aure dasu.”
Yace a yanzu haka yana zaune da matansa lafiya cikin kwanciyan hankalali kuma sun ɗauki junan su ‘yan uwan juna kuma abokan shawara.”