Labaran duniya

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Yanzu-Yanzu Atiku Ya Yanke Jiki Ya Faɗi An Garzaya Da Shi Ƙasar Waje

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Atiku Ya Yanke Jiki Ya Faɗi An Garzaya Da Shi Ƙasar Waje, Cewar FFK

Tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya bayyana cewa, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar na fama da rashin lafiya.

FFK ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, yace Atiku ya kamu da rashin lafiya ne bayan da ya koma Abuja daga Kaduna inda yayi yaƙin neman zaɓe.

A cewar FFK, Atiku yayi ƙorafin ciwon jiki inda ya yanke jiki ya faɗi.

FFK dai shine daraktan kamfe ɗin Bola Ahmad Tinubu da Shettima.

Ya ƙara da cewa, an fita da Atiku zuwa ƙasar Faransan dan neman magani.

FFK yace PDP na son ta yi rufa-rufa akan lamarin amma akwai abinda ke damun ɗan takarar shugaban kasarta wanda bata son ƴan Ni Nijeriya su sani.

Sai dai wata majiya ta kusa da Atiku ta ƙaryata hakan, inda tace kowa dai ya ga Atiku ƙalau jiya, dan FFK watakila ya sha wani abu ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN