Labaran Kannywood

Atiku ya Bankado Hujjoji Guda 10 da ake Tunanin zai zama Silar Sauke Bola Ahmad Tunubu

Da Dumi Dumi: Yanzu-Yanzu Atiku ya Bankado Hujjoji Guda 10 da ake Tunanin zai zama Silar Sauke Bola Ahmad Tinubu a Kotu kamar yadda zaku kalla a cikin wannan bidiyo dake kasa:

GADAI BIDIYON ANAN 👇

Jawabin da, Atiku Abubakar Ya gabatar kan Batun takardun Bogi da Yake zargin Tinubu yayi amfani dashi Ya Tsorata Yan Jam’iyyar APC Inda Wasu, Suka Fara Maganar Sashi 143. Na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Da Yace Idan Aka kama Shugaban da laifin da Yajanyo aka tsige shi za’a iya Rantsar da Mataimakin sa, a matsayin shugaban kasa.

Inaso Masu mafarkin za’a Rantsar da Kashim Shatima Idan kotu ta samu Tinubu da Wannan laifi suna Yaudarar Kansu ne.

Da majalissun tarayyar Nigeria ne suka bijiro da wannan Bincike da har Yayi sanadin suka tsige shugaban kasa to ana iya Rantsar da mataimakin sa, Amma Yanzu Dan takarar da yake kalubalantar sa ne Ya Bijiro da wannan Bincike Dan haka Muddin kotu ta same su da laifi zata sallame su ne tare.

MISALI.
Supreme court tayi amfani da matsalar takardun makaranta da ta kama Dan takarar Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa inda ta kwace kujerar gwamnan jihar Tabawa Dan takarar jam’iyyar Adawa kunga, ai ba gwamnan jihar takama da laifi ba Mataimakin sa takama da laifi tayi amfani da laifinsa ta hukunta su gaba dayansu ta hanyar kwace kujerar gwamnan jihar.

Amma lokaci ne kadai zai tabbatar da hukuncin da, Alkalan zasu Yenke Mudai fatanmu Allah Yasa muji Alheri.

Alkalamin. El-Usman Farawa.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN