Labaran Kannywood

BABBAR MAGANA: Yadda Wani Sabon Ango Ya Kwana A Banɗaki A Daren Farko

  1. BABBAR MAGANA: Yadda Wani Sabon Ango Ya Kwana A Banɗaki A Daren Farko

Wani ango ne bayan an kai amarya an yi musu kowa ya watse an bar Ango da Amarya bayan sun yi sallah sun ci abinci, sai ango ya ce wa Amarya bari in je in watsa ruwa in dawo, nan take Amarya ta raka shi ƙofar ɗaki.

Bayan ango ya gama wanka ya zo zai buɗe ƙofa sai ya ji an kulle ƙofar, ashe Amarya ce ta kulle shi ta baya.

Ko da ango ya ga haka sai ya kira sunan Amaryar ta zo don ta buɗe shi, amma Amarya ta na ji kawai ta yi kwanciyarta ta ƙyale Ango a kulle cikin banɗaki.

A haka dai Ango ya haƙura ya samu wuri ya kwanta cikin banɗaki har gari ya waye.

Da safe Amarya ta taso ta buɗe Ango ta durƙusa ta gaishe shi ta fara ba shi haƙuri kamar haka:

“Ka yi hakuri Angona, lallai na san cewa ban kyauta ma ka ba, dalili kuwa shi ne na yi wa tsohon saurayina alƙawarin duk wanda na aura a daren farkonmu a banɗaki zan bar shi ya kwana, kuma Alhamdulillah, na cika alƙawarin da na ɗauka.”

To fah…

Wai idan kai ne Angon ya zaka yi?

Ke mace ce, shin wannan Amaryar ta kyauta?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN