Labaran Kannywood
Babu Abunda yake Matukar Sani Bakin Ciki kamar Idan Na tuna Zan Mutu na koma ga Allah – Maryam Yahay
A sabuwar Shirin da BBC Hausa ke Gudanarwa wanda yayi mata Lakabi da “Daga bakin mai ita” shiri da bbchausa hausa take gabatarwa lokaci zuwa lokaci shirin shina za ana hira da mutane musamman mawaka da jaruman masana’antar Kannywood.
Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Yahaya yayin zantawa da BBC Hausa ya shaida cewa babu abinda ya fi bakanta mata rai kamar ta tuna cewa watarana zata mutu ta tarar da Allah.
Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne jarumar ta yi wani gagarumin ciwo wanda yasa ta fita daga hayyacin ta har wasu suka dinga tunanin mutuwa zata yi.
Ciwon ya yi matukar sauya mata halitta har ta kai ga wadanda suka san ta basa gane ta, yanzu haka dai ta warke sarai tamkar bata taba ciwo ba.