Bai Dace a Kori Safara’u ba a Kannywood dan Kawai Bidiyon Tsiraicinta ya Bayyana ~ Rahama Sadau
Hukuncin Korar Safara’u Kan Bidiyon Tsiraici A Kannywood Bai Dace Ba, Ni Da Aka Rika Kora Ta Dariya Na Rika YI, Cewar Rahama Sadau
Fitattacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta yi suka ga mahukuntan farfajiyar Kannywood kan dakatar da Safiya yusuf da suka yi a dallilin wani bidiyon tsiraicin ta da ya fallasa a shafukan yanar gizo.
Shahararren yar wasan finafinan kuma mawaƙiyar wacce aka fi sani da Safara’u ta bayyana cewa mata da dama suna ɗaukan kansu tsirara su ajiye a cikin wayoyin su.
Safara’u ta bayyana haka a hira da ta yi da BBC Hausa inda ta yi magana kan yadda ta ji a lokacin da aka fidda bidiyon tsiraicinta ya karaɗe shafukan soshiyal midiya.
Jarumar ta ce ba za ta iya faɗi ko sanin wanda ya saka bidiyon a yanar gizo ba.
” Waya ta ta kowa ce, ina ba mutane su yi amfani da ita wayar kuma ciki akwai bidiyoyin tsiraici na da yawa a ciki wanda nake ɗauka don nishaɗi in rika kallo. Shine aka cire wannan bidiyo aka yaɗa shi a shafukan sada zumunta.
Ta ce ko da aka gaya mata cewa ga bidiyon nan yana tashe a yanar gizo bata ji daɗi ba.
” Na samu tsangwama matuƙa sannan kuma ban ji daɗin abinda ya faru ba. Sai dai iyaye na basu muzguna min ba sun tausasa ni ne suka rika cewa in kwantar da hannu na.
” A harkar nishaɗantarwa kuwa buri na shine a ce yau na zama kamar Davido ko Burna Boy. In rika rangaɗa waka ina samun kyaututtuka kara waɗannan fitattun mawaka.
Sai dai kuma a wani bidiyo da jaruma Rahama Sadau, yi aka saka a facebook, ta bayyana cewa ba ta yi na’am ba da dakatar da Safara’u da MOPPAN ta yi ba, ta na mai cewa dakatarwar ba shine maganin ko gyara ba.
” Idan aka ce da zarar mutum yayi laifi sai a ce za a dakatar da shi ne , ni a gani na hakan ba shine zai gyara lamarin ba. Ma su hanzarin kora ko dakatar da jarumi ko jaruma don sun aikata laifi ba su yi musu adalci.
Rahama ta kara da cewa bayan ta kalli bidiyon da Safara’u ta yi na hira da BBC hausa, ta ga alamun tana cikin damuwa.
Ta yi kira da a nemo wani haryar hukunta wanda yayi laifi a Kannywood wanda ba da zarar mutum ya aikata laifi sai ace an kore shi.
” Ko lokacin da ka kore ni na farko, ni ban san wanda ya kore ni ba don ban san wanene yake korar ba. Duk lokacin da aka kore ni ko dakatar da ni daga Kannywood, ‘kecewa’ da dariya na ke yi, kawai in kama gaba na, don ko dadani da kasa baya yi.
Ta kara da cewa irin korar da ake yi wa mutane zai iya sa su afka cikin halin shaye-shaye da wasu matsalolin rayuwa