Labaran duniya

Bamu Amince da Tsarin Raba Maza Da Mata a Cikin aji ba ~ Zanga-Zangar Daliban Jihar Bauchi

Bamu Amince da Tsarin Raba Maza Da Mata a Cikin aji ba ~ Zanga-Zangar Daliban Jihar Bauchi

Daga Kamal Aliyu Sabongida

Yau Litinin 26/09/2022, Rana ce da aka koma makarantu a Jihar Bauchi kamar yanda hukumomi suka bada daman haka.

Jim kadan bayan komawa Makarantun, wasu daga cikin daliban sun mamaye manyan tituna a cikin garin garin Bauchi, suna bayyana wa Gwabnati rashin amincewar su da tsarin raba maza da mata da Gwamnatin jihar Bauchi tayi.

Na samu jin ta bakin wani ɗalibi wanda yaso na dakaye sunan shi, ko meye dalilin wannan zanga-zanga da sukeyi, ya bayyana mani cewa, lallai sunayi ne sabida rashin adalcin da aka musu na rabasu da abokan karatun su mata kenan, dan ya zama wajibi gwamnati ta duba wannan Lamari.

Idan ba a manta ba Gwamnatin jihar Bauchi dai, ta bijiro da tsarin raba Maza da Mata ne ta bakin Komishinan ilimi na jihar, Dr Aliyu Dilde, da nufin rage baɗala da yake afkuwa a tsakanin ɗaliban.

Tuni dai Jami’an ‘yan Sanda suka tarwatsa gangamin daliban, daga karshe kowa ya gudu izuwa gidan su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN