Labaran Kannywood

Batun Auren Jaruma Hadiza Gabon ta Girgiza Duniya

Batun Auren Jaruma Hadiza Gabon ta Girgiza Duniya

Batun Auren Jaruma Hadiza Gabon ta Girgiza Duniya

A cikin wannan satin aka fara yada wasu hotuna da bidiyon Fitacciyar jarumar Masana’antar Kannywood wato jaruma Hadiza Gabon tare da wani sharerren mai kudi wanda a cikin hoton sunyi fita irin amarya da Ango wanda hakan ta girgiza Masana’antar dama duniya baki daya.

Sai da alamun wannan maganar babu batun gaskiya a ciki dan Tun a baya wani labari yake yawo a kafofin sada zumunta cewa wai shahararriyar ‘yar wasan nanaye a masana’antar Hausa film Kanywood Hadiza Gabon ta fitar da bidiyo tana jawabin cewa tana son Maigirma Ministan Sadarwa Sheikh Dr Isa Ali Pantami da aure

Labarin yaci gaba da cewa, wai Hadiza Gabon ta shirya tuba da barin sana’ar gurbata tarbiyya ‘yan Arewa wato Hausa film muddin Malam Isa Ali Pantami ya amince zai aureta, wai ta gaji da sana’ar, aure take so, ance wai ta fitar da bayanin cikin bidiyo a shafinta na Instagram

Kamar yadda aka saba, Datti Assalafiy ya gudanar da bincike sosai kafin wannan rubutun, na ziyarci har verified Instagram account na Hadiza Gabon, kuma sakamakon binciken ya tabbatar da cewa babu wata kafar yanar gizo ko dandalin sada zumunta da ya nuna Hadiza Gabon tayi bayanin neman auren Malam Isa Ali Pantami da kanta ko ta umarci wani ya fada a madadinta, gaskiya babu

An yiwa Hadiza Gabon sharri ne kawai irin na yaran nan da suke bude jaridun bogi, wanda hakan har ya jawo wani zindiki a Bauchi ya yiwa Malam Isa Ali Pantami kazafi, yace wai Malam ai dama yana zuwa Dubai yana lalata da Hadiza Gabon, amma zamu baku labarin matakin shari’ah da aka dauka akan Zindikin da ya yiwa Malam kazafi nan da kwana uku zuwa biyu Insha Allah

Jama’a duk inda kuka ga labari don Allah ku gudanar da bincike kafin ku amince ko ku yanke hukunci, wato mun tsinci kanmu ne a wani irin mummunan yanayi na lalacewar aikin jarida a Arewa, wasu yara ne kanana suka koyi dabi’ar kirkiran jaridun bogi, suka samar da blog website na jaridun, sai su kirkiri labarin karya wanda zai ja hankali su saka don su sami kudi ta hanyar viewers daga Google AdSense

Don haka jama’a ku lura da wannan, kuma muna kira ga Gwamnati ta shigo cikin lamarin nan don daukar matakin shari’ah akan jaridun bogi, imba haka ba har yaki sai sun haddasa a cikin kasa ba da jimawa ba

Muna fatan Allah Ya tsare mana mutuncin Malam Is

-Datti Assalafy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN