Labaran duniya
Bayan Bacewar Tinubu a Najeriya Yanzu-Yanzu ya Iso Cikin Koshin lafiya
YANZU-YANZU: Tinubu ya dawo daga Landan
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar APC, Bola Tinubu ya dawo gida Nijeriya daga birnin Landan na Birtaniya a yau Alhamis.
Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan sadarwa ta zamani, ne ya bayyana hakan ta shafinsa na twitter a yau Alhamis.
Tinubu ya dawo Nijeriya bayan ya shafe kwanaki 12 a Landan, inda ake ta raɗe-radin ya je ne a duba lafiyarsa.
Rabon da a ga Tinubu a bainal jama tun 22 ga Satumba lokacin da ya gana da kungiyar Pentecostal bishops, inda har aka yi taron sa hannu na zaman lafiya kafin zaɓe amma ba ya nan.