Bello Turji Ya Maida Martani Kan Harin Boma Bomai Da Aka Kai masa
Kasurgumin Dan Bindiga Bello Turji Ya Maida Martani Kan Harin Jirgin Sojin Najeriya Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara Turji yace harin ya yi
sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni Ɗan bindigan ya yi gargaɗin cewa a shirye yake ya bi duk abinda gwamnati ta zaɓa tsakanin zaman lafiya da yaƙi Zamfara Ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, yace cin amana ne harin da Sojojin Najeriya suka kai sansaninsa a jihar Zamfara
yadda wani luguden wutan rundunar sojin saman Najeriya ya yi sanadin kashe gomman yan ta’adda a mafakar Turji. Bayanai sun nuna cewa ‘yan fashin dajin sun halarci wurin ɗaura aure tare da Bello Turji lokacin da jirgin NAF ya yi ruwan bama-bamai a wani yankin ƙaramar hukumar Shinkafi