Labaran duniya

Bidiyon Yadda Jami’an Nigeria Suka nunama Wancan Shegen Dan China Daya kashe Ummeeter cewa Lanjeriya ba kanwar Lasa bane

Yadda Jami’an Nigeria Suka nunama Wancan Shegen Dan China Daya kashe Ummeeter cewa Lanjeriya ba kanwar Lasa bane

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta tabbatar da kisan wata budurwa da wani ɗan ƙasar China, Geng Quanrong ya yi a Jihar Kano.

Rundunar, ta bakin kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce Quanrong ya kashe Ummukulsum Sani ta hanyar caccaka mata wuka har cikin ɗakinta a gidansu da ke unguwar Dorayi Babba a jihar Kano.

SP Kiyawa ya shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa dan Chinan, ɗan shekara 47, ya haura har gidan su ya rinyar ne ya kashe ta.

A na tunanin ɗan Chinan na zargin Ummukulsum da yaudarar sa, ta hanyar ƙin aurensa bayan ya daɗe ya na yi mata hidima.

Hakan ce ta Sanya ransa ya ɓaci, inda ya kuma ya je har gidansu da ke unguwar Yamadawa a Ƙaramar Hukumar Gwale, ya kuma kutsa har ɗakin marigayiyar ya kuma caccaka mata wuƙa har sai da ta ce ga garinku nan.

A cewar Kiyawa, bayan samun labarin ne Kwamishinan yan sandan Kano ya tura jami’ansa, karkashin DPO na Dorayi Babba, CP Abubakar Lawan in da su ka garzaya gidan da lamarin ya faru.

Ya ce da isarsu ne su ka ɗauki yarinyar zuwa Asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da da mutu.

Kiyawa ya ce tuni su ka damƙe wanda ake zargi kuma an mayar da shi shalkwatar rundunar domin ci gaba da bincike.

Bayan ya soka mata wukar ne kuma mahaifyarta ta yi ihun akawo taimako, inda wa ni matashi ya yi kukan kura ya kai ɗauki, inda daga ƙarshe a kai masa kofar rago a ka cafke shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN