Bidiyon Yadda Naburaska ya Karanta Hadisi a Maimakon Aya a yayin da yake Sallah a Saudiyya ya janyo Masa Cece-kuce a Duniya.
Wata Sabuwa! Bidiyon Yadda Naburaska ya Karanta Hadisi a Maimakon Aya a yayin da yake Sallah a Saudiyya ya janyo Masa Cece-kuce a Duniya.
Tofa! Naburaska Ya Fito da Sabuwar Sallah inda ya Karanta Hadisi a Maimakon Surah a yayin da yake Sallah.
Naburaska Yaushe Aka Fara Karanta Hadith A Cikin Sallah Oho?😳😳
GADAI BIDIYON 👇
Naburaska yayi jahilci.
Kwanakin baya nayi rubuce rubuce akan,yanda mawaki (Davido)yayi wanda takaima akayi masa chaa saboda yayi waka tare da sallah, saidai a wani bangaren nasake rubutu akan cewa wani abun mutanen mu na arewa sune suke nuna sallah kamar comedy,yanda zakaga wasu sunayi da sunanan comedy a aikin su.
Naci karo da video na dan kwankwansiya Naburaska yayi yaja aya kuma yaja hadithi,a wajen sallah dasunan yana addu’a wani abin takaici ma a kasa mai tsarki, wannan yana nuna maka tabbas naburaska bama ya iya banbance aya balle hadithi, mutane dadama sunyi tir,da Allah wadai domin wanda yasan yakoyi ibada bazai zo yana irin wannan shirmen banzan ba.
Kalli Bidiyon Anan 👇
Wannan kalubale ne garemu,idan ka lura a yanda naburaska yake jan ayoyin Alqur’ani din kasan bai iyaba,kuma baije ya koya ba, akwai irinsu kuma da malami yafito yana karatu ko wa’azi saikaga mutum na zagin sa, saboda jahilci,yanada kyau kowa yatashi ya nemi ilmi.Wallahi babu wani uzuri dazaka koma wajen Allah kace baka zuwa neman ilmin addinin musulunci,abun kunya ma ace karatun Alqur’ani.