Labaran duniya

Bidiyon Yadda wasu yan ta’adda suka kai hari har gida dan garkuwa da wani mutum a funtua

NIGERIA A YAU

Kamar yadda zaku gani a bidiyo, daren yau da ya gabata da misalin karfe 10:20pm masu garkuwa da mutane suka shiga gidan wani Electrical Engineer a garin Funtua jihar Shugaban Kasa da niyyar zasu sace shi

Allah Ya sa mutumin baya gida tare da iyalansa, masu gadin gidansa sun tsere, ‘yan ta’adda sun samu nasaran karya kofar gate suka shiga gidan, amma basu iya balle kofar shiga cikin falo da dakuna ba

Shi kuma Maigidan ya kafa CCTV Camera suna nadar faifan bidiyo na duk abinda yake faruwa a gidansa ko da baya nan, domin ya hada CCTC Camera din da Handset dinsa

Kuma wannan ne abinda ya faru, baya gida amma yana kallon duk abinda yake faruwa saboda yayi connecting da wayarsa, sun fita daga gidan, suka shiga wata unguwa da ake kira Project Quarters Funtua suka kwashi mutane da yawa suka tafi dasu jeji

Abin takaici shine a irin wannan yanayi ko ka kira jami’an tsaro baka da tabbacin za’a kawo maka dauki

Ya kamata ‘yan Arewa muyi karatun ta nutsu, kar mu bari a sake yaudaran mu, mu duba shugabanni da suka cancanta, sannan mu dage da addu’ah da tuba

Allah Ya karemu gaba daya

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN