Labaran duniya

Budurwa Ta Saya Wa Mai Gadinta Takalmin Naira Miliyan 1 Don Yasa Ya je Masallacin Juma’a

Budurwa Ta Saya Wa Mai Gadinta Takalmin Naira Miliyan 1 Don Yasa Ya je Masallacin Juma’a

Shahararriyar mai zanen nan, kuma tsohuwar budurwar shugaban ƙungiyar direbobi ta Legas MC Olumo, wato Ehi Ogbebor, ta gwangwanje mai gadinta da takalma ƙirar ‘Louis Vuitton’ da ta saya akan kuɗi Dalar Amurka 1000 kwatankwacin Naira Miliyan ɗaya da ɗoriya.

Karamcin da Ehi Ogbebor ta yi wa mai gadin nata ta haifar da ce-ce-ku-ce a yanar gizo inda wasu ke cewa kamata yayi ta bashi kuɗin a maimakon ta siya masa wannan takalmin mai ɗan karen tsada.

A cikin wani faifan bidiyon, an ga Ehi tana addu’a ga mai gadin gidanta tare da yaba masa bisa jajircewa wajen gudanar da aikinsa. A cewar ta, wasu mutane suna raina masu aikin gidansu da sauran ma’aikatan gida duk da cewa ayyukansu ba su da sauƙi.

Ta ce ta siya wa mai gadin nata takalmin ne domin yayi ado da shi a ranar juma’a ya tafi da shi masallaci domin yin sallar Juma’a, inda tayi addu’a tare da fatan Allah ya daɗa mata ɗaukaka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN