Cikekken Tarihin Rayuwar Alhaji Aliko Dangote
Cikekken Tarihin Rayuwar Alh. Aliko Dangote, Gidansa ýayansa, Matarsa, Motar da yake Hawa, Kamfanoninsa da Sauransu.
GA CIKEKKEN BAYANI DAGA BAKIN MAI ITA
HAIHUWA
An haifi Aliko Dangote ne a Afrilun 1957 a cikin Garin Kano. Mahaifin sa Muhammad Dangote, babban ‘dan kasuwa ne kuma ‘dan siyasa a lokacin jamhuriya ta farko wanda ya rasu tun Dangote yana karami.
Mahaifiyar sa Mariya Jika ce a gidan Alhasawa watau dangin Alhassan Dantata, wanda har yau tana raye.
KALLI BIDIYON GIDAN ALHAJI ALIKO DANGOTE 👇
KARATU
Aliko Dangote yayi karatun addinin Musulunci da kuma Boko a Kano, har ya zarce zuwa babbar jami’ar nan ta Al Azhar da ke kasar Masar inda ya karanta ilmin kasuwanci ya kuma kare yana shekara 21.
KASUWANCI
Aliko Dangoye ya samu jarin da ya fara kasuwanci ne daga hannun Baffan sa a 1977. Tun kafi wannan lokaci, Aliko Dangote ya nuna sha’awar sa ta harkar kasuwanci da ya gada daga dangin Mahaifiyar sa. Daga baya abubuwa sun budawa Aliko Dangote inda yayi kaimi a lokacin mulkin Obasanjo ta hanyar wani na-kusa da shi. Dangote ya rika jigilar kasuwanci zuwa kasashen waje tun kafin rasuwar Kakan sa.
KALLI JIRGI DA MANYAN MOTOCI DA DANGOTE KE HAWA👇
KAMFANIN DANGOTE
Daga baya Dangote ya bude kamfanin sa da ya radawa sunansa, bayan ya gawurta. Aliko Dangote ya daina harkar dillanci a 2005, inda ya koma hada taliya, fukawa, sukari, gishiri da siminti na kan sa ba tare da sayo na waje ya saida ba.
DUKIYAR DANGOTE
Yanzu dai Dangote yayi kaimi a kaf Duniya inda ya zama bakin mutumin da ya fi kowa arziki. Forbes tace Dangote ya ba fiye da fam Dala 10 baya kuma yana cikin manyan Attajiran Duniya a halin yanzu.