Labaran duniya

Cikin fushi da Bacin Rai Buhari yayi zazzafan martani akan kisan gillar da Kayiwa Sheikh goni Aisami

Cikin fushi da Bacin Rai Buhari yayi zazzafan martani akan kisan gillar da Kayiwa Sheikh goni Aisami

Cikin fushi da bacin rai shugaban kasar Nigeria yayi zazzafar martani akan kisan gilla da akayiwa fitaccen malamin addinin musulunci watoh Sheikh goni Aisami.

Shugaban ya Bada Umarni akan a Binciko wadanda sukayi wannan aika aika cikin gaggawa kuma a Yanke musu hukunci dai dai da abunda suka aikata.

TUNI AKA KORESU DAGA AIKIN.

Rundinar sojin Nigeria ta kori sojoji guda biyu wadanda ‘yan sanda suka kama da laifin aikata kisan kai da fashi da makami

Sune sojojin da suka harbe babban Malamin Musulunci a jihar Yobe Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da yunkurin sace motar Malamin

Sojojin masu mukamin Lance Corporals wato Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Gideon Adamu, amma kafin a koresu daga aiki sai da aka rege musu matsayi zuwa kuratan Sojoji wato Private

Laftanar Kanar Ibrahim Abdullahi Osabo shine Mukaddashin Kwamandan Recce Battalion rundina ta 241 dake da sansani a garin Nguru jihar Yobe inda sojojin suke aiki ya gabatar da korarrun sojojin, sannan ya mikasu wa ‘yan sanda domin a gurfanar da su a Kotu

Aladu sun kashe ragon layya, tabbas ba zasu tsira ba

Muna fatan Allah Ya tabbatar musu da mafi tsananin hukunci
Allah Ya karbi shahadar Sheikh Muhammad Goni Aisami

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN