Labaran duniya

DA ƊUMI ƊUMI: Sheikh Ibrahim Zakzaky da uwargidansa sun shilla waje neman lafiya

DA ƊUMI ƊUMI: Daga Karshe dai Sheikh Ibrahim Zakzaky da uwargidansa sun Samu daman shilla Kasar waje neman lafiya.

Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.

A wani rahoto da muke samu daga wasu majiyoyi masu tushe cewa jagoran harkan musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky tare da uwargidansa Zinatuddeen Ibrahim Zakzaky sun bar Nijeriya domin fita ƙasar waje neman Lafiya.

Bugu da ƙari hakan ya biyo bayane bayan sakarwa shehin tare da uwargidan nasa fasfo ɗin su da gwamnatin tarayya ta yi a makon da ta gabata.

Riƙe fasfo ɗin nasu ya biyo bayane tun bayan wankesa da kotun tarayya dake kaduna ta yi dangane da wasu tuhume-tuhume da gwamnatin jihar kaduna ƙarƙashin tsohon gwamnan maigirma Nasir Ahmad Elrufa’i ke yi masa.

Cika hannu da babban shehin da gwamnatin jihar kaduna ta yi yana da nasabar yadda tun bayan dirar mikiya da sosojin Nijeriya suka yi akan mabiyansa a garin Zariya a shekarar 2015, “inda aka yi asarar dubbannan rayuka da kuma rushe duk wasu muhimman wuraren Ibada na mabiya mazhabin Shi’ar a garin zariya jihar kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN