Labaran duniya

DA ƊUMI-ƊUMI- ‘Yan kwana-kwana Sun gano Sassan jikin Mutane a wata Mota a ilorin

DA ƊUMI-ƊUMI- ‘Yan kwana-kwana Sun gano Sassan jikin Mutane a wata Mota a ilorin.

Daga Rafi’atu Mustapha Katsina.

‘Yan kwana-kwana na jihar kwara Sun ce Sun gano wasu Sassan jikin Mutum biyu tare da Mota Can kasan ruwan teku a Akerebiate Cikin ilorin.

Shugaban Sashen media da jama a, Mr hassan Adekunle, yayi wannan bayanin a jiya asabar a Ilorin.

Yace jikin Mutane biyun da motar Toyota Yaris Mai dauke da lambar rijister: APP544E, an gano sune a cikin teku dake kusa da Olusola Saraki Abattoir a Ilorin.

‘Yan jita-jita Sunce lamarin ya farune a daren ranar juma’a lokacin da ake ruwa, a lokacin da Masu tafiyar Suke ta kokarin ganin Sun tuka motar domin tafiya amma Sai ruwa ya jasu ya tura su Cikin tekun.

Maganar gaskya Masu aikin taimakon kamar wani hadin gwiwa ne da Suka hadu Sukayi aikin tare, Saboda dukkan mutanen dake makotaka da wajen Sun bada Cikakkiyar gudunmuwa domin taimakawa ‘yan kwana-kwanan dan gudanar da aikin, inji Adekunle.

Dan haka ya bada Shawara ga dukkan al-umma akan Su guji tuki Cikin ruwa mai tafiya.

Ya kara da cewa wadannan gawarwaki har yanzu ba asan daga ina suke ba ba a san su waye ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN