Da Dami Duminta: Yanzu-Yanzu Sarkin Waka Ya Saki Zazzafar Wakar Malam Isah Ali Pantami wanda ya Girgiza Duniya
Da Dami Duminta: Yanzu-Yanzu Sarkin Waka Yayiwa Isah Ali Pantami Waka Mai Zafi.
Fitaccen mawakin Hausa wato Naziru wanda akafi sani da Sarkin waka ya Raira Wata waka ga Malamin addinin Musulunci Sheikh Isah Ali Ibrahim Pantami.
Wanda wakar ya mutuwar Jan Hankalin Mutane saboda yadda Malam yake haramta wakoki a cikin tafsirinsa, yau kuma gashi shi akayiwa wakar kai tsaye.
GADAI WAKAR:
Mutane da yawa sun shaida cewar Malam bazai yarda acigaba da yada wakar ba, sai dai tuni wakar ta zagaye duniya awanni kadan bayan fitowar wakar. Wanda a yanzu haka muna dauke da wakar zamu saka muku ku saurara.
Gadai wakar a Kasa
Shehin Malami Mai Tarin Ilmin Da Ya Kafa Tarihi A Nahiyar Afrika
Daga Comr Abba Sani Pantami
√ Shine Dan Afrika na farko da ya taba zama shugaban tsangayar koyon rubutun musulunci a Jami’ar Madina a shekarar 2014.
√ A cikin kasa ga shekaru uku ya nuna irin bajintar sa inda ya samu kyaututtukan girmamawa guda dari da goma (110) a ciki da wajen Nijeriya.
√ Haka kuma ya samu kyautar mutum mai kwazon daukaka ko samar da cigaban harkar sadarwa ta zamani wato ICT Promoter a turance a shekarar 2017 a Birnin London.
Sunan wannan bawan Allah shine: Sheikh Dakta Isah Ali ibrahim Pantami
Ya samu Digiri da shaidar karatu kamar haka:
– Digirin farko wato Bsc akan hakar Na’ura mai kwakwalwa (Bsc Computer) a Jami’ar ATBU dake garin Bauchi
– Yayi Digiri na biyu wato Msc a turance a fannin ilimin Na’ura mai Kwakwalwa a Jami’ar ta ATBU (Msc Computer)
– Ya samu takardar shaidar MBA Technology a Jami’ar ATBU dake Bauchi
– Ya samu Digirin Digirgir wato Ph’D Oil and Gas Computing a kasar England
– Ya samu Digiri a fannin samar da sauye-sauye a fannin yanar gizo wato Digital Transformation a Jami’ar Harvard
– Ya samu shaidar strategic innovation a MIT, dake kasar Amurka (USA)
– Ya samu takardar shaidar Management a Jami’ar Cambridge, dake USA
– Ya koyar a Jami’ar ATBU dake Bauchi
– Ya zama babban Darakta na hukumar NITDA a Nijeriya
– Ya zama Ministan sadarwa da kuma tsare-tsaren tattalin arziki na zamani wato Communication and Digital Economy a Turance
– Babban mahaddacin Qur’ani ne
– Babban mai wa’azi da fassarar alkur’ani ne
Muna Addu’ar Allah ya yi maka jagora, ya baka ikon sauke nauyin da aka daura maka, yaa Hayyu Yaa Qayyum.