Labaran duniya

DA DUMI-DUMI: An Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU

Lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana ya ce nan ba da jimawa ba za a kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ke yi.

Falana, wanda kuma shi ne lauyan kungiyar ASUU, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da wani littafi da Lanre Arogundade, mai suna “Breaking Coconut with Your head,” a Events Centre, Agidingbi, Legas.

Sai dai Falana ya ce ba zai iya bayyana yadda za a warware yajin aikin na watanni 8 ba saboda sirri.

A baya ma dai game da Yajin aikin ASUU, Kotun Daukaka Kara ta umurci Malamai da su gaggauta komawa bakin aiki, to amma sun zargi Ngige kan cewar yana dagula tattaunawar FG da ASUU.

Kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta umurci kungiyar da ke yajin aiki da su koma aji.

Kotun ta bayar da umarnin ne bayan ta yi watsi da bukatar kungiyar ta dakatar da aiwatar da hukuncin da kotun masana’antu ta kasa ta yanke a baya na umurtar malaman jami’o’in da su koma bakin aiki.

Da yake magana kan halin da kasar ke ciki, Falana ya ce Najeriya ta lalace kuma akwai bukatar a sauya injinta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN