Labaran duniya

Da Dumi Dumi: Yan Ta’adda Sun Saki Cikekken Bidiyon yadda suka Harbo Jirgin Sojojin Najeriya

Yanzu Yanzu: Yan Ta▪︎Adda Sun Saki Yadda Suka Harbo Jirgin Yakin Sojojin Najeriya.

Hotunan yadda ‘yan ta’*adda masu Garkuwa da Mutane, suka harbo jirgin yakin Sojojin Najeriya a kauyan Chukuba da ke karamar hukumar Shiroro jihar Niger, kamar yadda na baku labari tun a shekaran jiya.

Tun a shekaran jiya da dare mutanan dake yankin da abun ya faru suka shaida mun da cewa Dogo Gyade ne da yaranshi suka harbo jirgin yakin Sojojin Najeriya, tare da kone jirgin kurmus.

Na saka wani bidiyo a fostin dina kafun wannan, zaku iya dubawa kuga yadda suke bayani da izzah a wurin da suka harbo jirgin ya fado, a shekaran jiya da na sanar muku da wannan labarin, Mutane da dama sun karyatani har wasu manya sai da suka mini magana akan labarin karya ne, bayan ni kuma na yadda da mutanan da suka tabbatar mun da cewa tabbas haka zancen yake.

GADAI BIDIYON 👇

PLAY

Abunda yafi bani takaici yadda suke Kabbara a cikin bidiyon tare da nunawa Duniya cewa su aikin Allah suke yi, kuma fa Garkuwa da Mutane ne aikin su da kashe Mutane, Allah ya kyauta.

Wai yanzu a Najeriya ashe har ‘yan bindiga sunyi karfin da zasu iya harbo jirgin yakin Sojojin Najeriya, tare da ka*she kowa dake cikin jirgin, wallahi idan ba’a dauki mummunan mataki akan su ba, nan gaba har jiragen da bana sojojin ba, zasu fara harbowa.

Har zuwa yanzu Gwamnatin kasar ta kasa fitowa ta bayyanawa duniya ainahin gaskiyar yadda lamarin yake. Allah ya kyauta.

✍️ Comr Abba Sani Pantami

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN