Labaran duniya

Da DUMI-DUMI Yanzu Yanzu Bidiyon Gawar Shekau Shugaban Boko-Haram ya Bayyana bayan ya Hallaka kanshi da Bom da jimawa

Bidiyon Gawar Shekau Shugaban Boko-Haram ya Bayyana bayan Bom ya Tashi dashi Har Lahira

Shugaban ya Bindiga Abubakar shekau shine shugaban yan Boko-Haram da suka Addabi Arewacin Najeriya.

Shekau ya Tada Bom ne ya kashe kansa dan gudun kada Akama shi hannu da hannu, wanda hakanne yasa akan rasa samun ko gawarshi, sai dai ayau wani bangare na Sassan jikinsa ya bayyana wanda ayanzu zamu nuna muku ita.

Gadai Bidiyon

Kuyangu 83 Sheƙau Ya Mutu Ya Bari A Duniya

Wasu Kwamandojin kungiyar Boko Haram sun ce tsohon jagoran kungiyar, Abubakar Shekau, ya mutu ya bar kuyangu 83 kafin ya bar duniya.

Majiyar Focus News Hausa, Aminiya ta rawaito cewa Shekau ya rasu ne a watan Mayun 2021, yayin wata arangama da wata kungiyar ’yan ta’addan a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

To sai dai da yake jawabi a Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, mai ba Gwamnan jihar shawara kan al’amuran tsaro, Birgediya-Janar Abdullahi Ishaq, ya ce wasu daga cikin makusantan Shekau din ne suka ba shi labari a kan kuyangun bayan sun mika wuya.

Ya ce, “Mun fara neman hanyar maganin ‘yan ta’adda ta ruwan sanyi kimanin wata 16 da suka wuce, jim kadan da mutuwar Abubakar Shekau, kuma gwamnati ba ta son ISWAP ta ci gaba da amfani da mayakansu. Mun san hakan na da matukar hatsari.

“Amma daya daga cikin mayakan da muka karba a Bama, ya shaida mana cewa Shekau ya mutu ya bar kuyangu 83. Ku ji fa, wai kuyangu 83!

“Sun ce yanzu haka yana wuta saboda ya aikata zunubi yayin arangamarsu da daya bangaren. A kullum yakan fada musu su fita su yi yaki, idan aka kashe su, ’yan matan Aljanna na jiransu,” inji shi.

Ya kuma ce mayakan da dama sun yi nadamar bin Shekau din, inda suka ce ya batar da su.

Birgediya-Janar Abdullahi ya kuma ce da yawa daga cikin mabiya Shekau din ko Alwala ba su iya yi ba, ballantana Sallah, sai da suka dawo da su Maiduguri sannan suka koya musu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN