Da DUMI-DUMI: Yanzu Yanzu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya Bada Umarnin kowanne dan Tijjaniyya ya Zabi Atiku Abubakar a Masayin Shugaban Kasa
Fitaccen malamin addinin Musluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya ce shi fa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai goya wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar mai zuwa, domin kuwa shi mutanensa za su zaɓa.
Shehin malamin ya bayyana haka ne a cikin wani gajeren bidiyo da Labarai24 ta tabbatar da sahihancinsa.
GADAI BIDIYON 👇
“Assalamu alaikum, Allah ya kawo mu lokacin zaɓe jama’ar ƙasa, ‘yan uwana ‘yan Najeriya.
“Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana cewa bai kamata a ciji mumini a rami ɗaya ba. Abu ya cije ka a wannan ramin, gara ka canja hannunka.
“Saboda haka na ji waɗansu mutane suna cewa a zaɓi wanda za a zaɓa ya ɗora mana akan inda muka tsaya. To ai inda muka tsayan ba daɗi muka ji ba ballai mu ɗora akai.
“Mutum sai ya ji daɗi yake ce a ƙara mini. In bai ji daɗi ba kam ba ya cewa a ƙara mini. Saboda haka ina wa’azi, ina kira, ina bada shawara a zaɓi yadda za a samu canji ko Allah zai canza mana.
“Inda muka tsayan ba mu ji daɗi ba balli a ɗora akai”, in ji Shehi.
“Ya ku jama’ar Najeriya ‘yan uwanmu ‘yan ƙasa, ga zaɓe ya zo, muna kiran ku, mutanena sun ce su Atiku za su zaɓa, ni kuwa ba zan rabu da mutanena ba.
“Saboda haka, Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Allah ya kiyaye mu ya kiyaye mana ƙasarmu, ya ba mu kwanciyar hankali.
“Zan nanata, ni mutanena da suke yin siyasa sun ce su Atiku za su zaɓa. Tun da ga wanda za su zaɓa ni ba zan rabu da su ba, ina tare da su. Zan tsaya tare da su mu ga abin da Allah zan yi. Allah ya zaɓa mana alheri”, Shehi ya ƙara da haka.