Labaran duniya

Da Dumi duminsa Sojojin Juyin Mulki Gabon Sun Bayyana Shugaban Su Yanzu-Yanzu

Da Dumi Dumi 🔥🔥🔥🔥 Yanzu Sojin Mulkin Gabon Sun Bayyana Bidiyon Sabon Shugaban da suka nada

Yau sa Asuba Sojoji sukayi juyin mulki a kasar Gabon..!

An hambare Gomnatin Ali bango odimba Shugaban Kasan gabon.

Wasu manyan hafsoshin soji sunje gidan talabijin na kasa a Gabon suna cewa sun kwace mulki ne saboda zaben da aka gudanar a karshen mako bai dace ba. Kuyi kokari kuyi Following Bala Sale Domin samun Labarin Dalla Dalla yadda Abun yafaru.

Jami’an, wadanda suka bayyana a Gabon24 da sanyin safiyar Laraba, sun ce sun soke zaben, sun rusa dukkan hukumomin gwamnati tare da rufe iyakokin kasar…..

Sun ce suna wakiltar dukkan jami’an tsaro da tsaro na Gabon.

GADAI BIDIYON 

Me Za Mu Sani A Takaice Game Da Kasar 🇬🇦 Gabon?

1. Asalin sunan kasar a gwamnatance shi ne Gabonese Republic.

2. Ba ta cikin ECOWAS, domin ECOWAS kasashe ne na yammacin Afirka.

3. Tana kudu da 🇳🇬 Nigeria, kasar 🇨🇲 Kamaru ita ta raba tsakanin Gabon da Nigeria.

4. Ita Gabon ba a yammacin Afirka take ba, shi yasa ba ta cikin ECOWAS, ita tana tsakiyar Afirka ne (Central Africa), a tsakiyar Afirka din tana gaɓar ruwa ta yammacin tsakiyar Afirka.

5. Mutanen kasar ba su wuce mutum miliyan 2 da dubu dari uku ba. Kenan ba su kai jihar Gombe ba ma.

6. Libreville shi ne babban birnin kasar, kuma shi ne gari mafi girma a kasar.

7. Yaren French shi ne yaren kasar a gwamnatance.

8. Samada rabin yan kasar Kiristoci ne, sai kuma Musulmai masu biye da su.

9. Ali Bongo Ondimba shi ne shugaban kasar da aka hambare, kuma ya fara mulki tun shekarar 2009, shekaru 14 baya. Wannan shi ne tazarcensa na 3 wanda sojoji suka masa juyin mulki da cewar ba bu adalci a zaben.

10. Kasashen da suke tsakiyar Afirka (Central Africa) su ne; 🇦🇴 Angola, 🇧🇮 Burundi, 🇹🇩 Chad, 🇬🇶 Equatorial Guinea, 🇨🇲 Cameroon, 🇨🇫 Central African Republic, 🇨🇩 Democratic Republic of the Congo, 🇷🇼 Rwanda, 🇸🇹 Sao Tome and Principe, 🇨🇬 Republic of the Congo, sai kuma ita 🇬🇦 Gabon din.

11. Su nasu kungiyar wacce take irin ta ECOWAS ana kiranta da ECCAS (Economic Community of the Central African States).

Wanda ya rubuta
Abu Albani Auwal Ahmad

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN