Labaran duniya

DA DUMIDUMINSA: Bello Turji Ya Soma Kaddamar Da Hari Akan ‘Yan Bindigan Zamfara, Bayan Gwamna Matawalle Ya Masa Afuwa

DA DUMIDUMINSA: Bello Turji Ya Soma Kaddamar Da Hari Akan ‘Yan Bindigan Zamfara, Bayan Gwamna Matawalle Ya Masa Afuwa

Bello Turji ya kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Bello Turji, wanda Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai da wata jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.

Hassan ya yabawa Turji bisa matakin da ya dauka na ajiye ayyukan fashi da makami, da kuma matakin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a kananan hukumomi uku da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

A cewar mataimakin gwamnan, tun makwanni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi na jihar ba, sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar.

Gidan talibijin na Channels ya ruwaito mataimakin gwamnan na cewa, kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya jagoranta ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin ‘yan bindiga tara a gundumar Magami da Masarautar Dansadau na kananan hukumomin Gusau da Maru na jihar domin su daina kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ci gaba da cewa, Turji wanda Gwamna Bello Matawalle ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN