DA DUMIDUMINSA: Zan Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Nasarar Tinubu, Cewar Atiku
DA DUMIDUMINSA: Cikin Fushi Da Bacin Rai Yanzu-Yanzu Atiku ya Bayyana Zai Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Nasarar Tinubu.
Gadai Bidiyon
Tabbas Anyiwa Zaben 2023 Mummunan Fyade Ta Hanyar Dannewa Yan Nijeriya Hakkin Su Na Tabbatar Da Wanda Suka Zama Ta Hanyar Na’urar BVAS A Lokacin Zaben 2023, Cewar Atiku Abubakar
Wato jama’a jagoran tabbatar da adalci a cikin Nijeriya kuma dan takarar neman mulkin Nijeriya na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya yi taron manema labarai na duniya inda ya gabatar da matsayar sa akan babban zaben shugaban kasa na 2023 wanda ya gudana a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu 2023.
Atiku Abubakar ya yi jawabai masu matukar sosa zuciya a gaban manema labarai na duniya inda ya tabbatar da cewa zai nemi hakkin yan Nijeriya a kotu domin ya tabbatar da cewa kotu zatama yan Nijeriya adalci ta hanyar basu wanda suka zaba.
Ga jawabin Atiku Abubakar a takaice.
(1) Sama da shekaru 30 nake yaki domin tabbatar da tsarin mulkin Demokaradiyyah a Nijeriya tare da kalubalantar ‘yan jari hujja wanda suka mayar da Nigeria baya tare da danne hakkin ‘yan Kasa
(2) An yiwa rayuwana harin ta’addanci a garin Kaduna tare da Babban Yarona Adamu domin a kashe ni, mun tsallake harin, amma wasu daga cikin ‘yan sanda da suke tare damu sun rasa rayuwarsu
(3) Ina daga cikin wadanda suka yaki tsarin mulkin sojoji, na bada gudunmawa wajen tabbatar da nasaran MK Abiola wanda shima a karshe ya rasa rayuwarsa sakamakon yunkurin da muke wajen ceto Kasarnan daga mawuyacin halin da take ciki tsawon shekaru
(4) A kokarin da nake don tabbatar da mulkin adalci a Nigeria, an yiwa rayuwana harin ta’addanci don a kashe ni yafi sau a kirga, anyi kokarin ruguza harkokin kasuwanci ne, har sai da ta kai nayi gudun hijira don neman mafaka
(5) Ni ne na jagoranci dakile tazarcen Obasanjo wanda da yanzu babu batun Mulkin Demokaradiyyah, nayi hakane domin a bawa kowa dama a Kasa cikin tsarin mulkin Demokaradiyyah
(6) An gudanar da zaben Shugaban Kasa na 2023, zabe ne wanda yake cike makil da magudi da cin amana, zabe ne na rashin gaskiya, an yiwa tsarin mulkin Demokaradiyyah mummunan fyade
(7) Ba’a aiwatar da tsarin dokar zabe na Kasa da akace za’ayi amfani da na’urar BVAS ba, sai aka karbi sakamo a takarda kawai, maciya amana sun rubuta abinda suka ga dama na sakamakon zabe, Shugaban hukumar zabe ya biye musu, Shugaba Buhari bai cika mana alkawari na cewa zai bari a gudanar da zabe na adalci ba
(8) Wakilan Majalisar dinkin duniya sun kalli sakamakon zaben, sun tabbatar da cewa ba’a bi ka’ida wajen karban sakamakon zabe na gaskiya ba, saboda ba’ayi amfani da na’urar BVAS wanda ta tantance masu kada kuri’a ba
(9) A zauna lafiya, ban amince wani daga cikin masoyana ya tada hankali ko rigima ba, mu guje wa duk wani mataki na tayar da hankali
(10) Zamu bi hakkin jama’ar Nigeria a Kotu, muna kyautata zato zamu samu adalci a Kotu, ba ina neman mulkin Nigeria don biyan bukatar kaina bane, inayi don al’ummah ne, dole a kwato hakkin al’umma.
Mu kuma muna rokon Allah akan ya taimaki Atiku Abubakar akan kyawawan manufufin shi na alkairi.
Ga Cikakken bayanin Cikin Bidiyo