Kannywood
Daddy Hikima (Abale) ya Angonce da sabuwar Mota wadda babu mai irinta a kaf Kannywood
Daddy Hikima (Abale) ya Angonce
da sabuwar Mota wadda babu mai
irinta a kaf Kannywood
Fitaccen jarumin nan wanda tauraruwar sa take haskawa Daddy Hikima wanda wasu sukafi sani da suna Abale ko kuma Ojo ya angwance da sabuwar motar shi wadda babu mota mai kirar tashi a kaf cikin masana’antar Kannywood a yayin da ake daf da shiga watan Ramadan mai Alfarma na 2022.
Ko a kwanakin baya mun bayyana muku cewa Jarumin yana daya daga cikin jaruman Kannywood da sukafi samun kudade a cikin masana’antar ta Kannywood
a shekarar 2021 zuwa 2022.
Ga dai Bidiyon motar kamar yadda
tsohuwar jaruma Rashidat Mai Sa’a ta wallafa a shafin ta na Instagram.