Labaran Kannywood
Daddy Hikima (Abale) ya Angonce da sabuwar Mota
Daddy Hikima (Abale) ya Angonce
da sabuwar Mota wadda babu mai
irinta a kaf Kannywood
Fitaccen jarumin nan wanda tauraruwar sa
take haskawa Daddy Hikima wanda wasu
sukafi sani da suna Abale ko kuma Ojo ya
angwance da sabuwar motar shi wadda
babu mota mai kirar tashi a kaf cikin
masana’antar Kannywood a yayin da ake
daf da shiga watan Ramadan mai Alfarma
na 2022.
Ko a kwanakin baya mun bayyana muku
cewa Jarumin yana daya daga cikin
jaruman Kannywood da sukafi samun
kudade a cikin masana’antar ta Kannywood
a shekarar 2021 zuwa 2022.
Ga dai Bidiyon motar kamar yadda
tsohuwar jaruma Rashidat Mai Sa’a ta
wallafa a shafin ta na Instagram.