Labaran duniya

Dalilin Da Ya Sa Na Jefe Ƴaƴana Biyu Har Lahira, Cewar Wani Mahaifi Da Ya Kashe Ƴaƴansa

Dalilin Da Ya Sa Na Jefe Ƴaƴana Biyu Har Lahira, Cewar Wani Mahaifi Da Ya Kashe Ƴaƴansa

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Wani mahaifi ɗan shekara 25 a jihar Adamawa, Elisha Tari, ya bayyana dalilin da ya sa ya jefe Ƴaƴansa biyu da duwatsu har lahira a makon jiya. Ya ce ya jejjefe yaran ne saboda rashin biyayyarsh.

Na tambaye su su ce ‘Allah’ amma sai suka ce ‘wuta’ maimakon haka, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ƴan sanda da ke Yola inda ake tsare da shi kan lamarin. A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne aka damƙe ɗan asalin ƙauyen Himike da ke ƙaramar hukumar Michika bisa zarginsa da jefe Ƴaƴansa biyu da duwatsu, har suka mutu. Elisha mawaƙin gida ne wanda matarsa ​​ta tafi, ta bar masa ƴaƴan biyu.

Da yake zantawa da manema labarai yayin da ake gabatar da su tare da wasu mutane 30 da ake zargin, Elisha ya ce yaran sun zo wurinsa a kicin ne a ranar da yake dafa musu abinci.

Ya ƙara da cewa har ya kai ga tambayarsu su ce ‘Allah’ amma sai suka ce ‘wuta’ suka riƙa maimaita ‘wuta’, ‘wuta’ maimakon su ce ‘Allah’. Na fusata da matakin da suka ɗauka, sakamakon haka na ɗauko duwatsu na jejjefesu a kai,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN