Labaran duniya

Dalilin da yasa aka sauke Abba kabir Yusuf a karagar Mulki

A ranar Laraba 20 ga watan nan na Satumba ne kotun wadda ta saurari ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar inda ta kalubalanci nasarar da hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ayyana ta zaɓen Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris na 2023 ta soki nasarar.

Kotun wadda ta gabatar da hukuncinta ta manhajar Zoom a Cikin Bidiyo ta ce tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne ya ci zaɓen Kamar yadda zaku gani a Cikin wannan Bidiyon:

GADAI BIDIYON 👇

PLAY VIDEO

Ta ce ta soke ƙuri’a 165,633 da ta ce aringizo ne aka yi wa ɗan takarar jam’iyyar NNPP, wanda tun farko hukumar zaɓe ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.

A ranar 29 ga watan Mayu, na 2023 ne aka rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

‘Ba zamu karaya ba’
Injiniya Abba Kabir ya ce ko kaɗan hukuncin ba zai rage musu ƙwarin gwiwa ko ya sanyaya musu gwiwa ba a kan yadda suke gudanar da ayyukansu ga al’ummar jihar ta Kano ba.

YADDA ABBA GIDA-GIDA YAYI CIKEKKEN BAYANI AKAN TSIGESHI DA KOTU TAYI👇

PLAY ▶️

Gwamnan ya bai wa al’ummar da suka zaɓe shi tabbacin cewa kotun ɗaukaka ƙara wadda suke da damar garzayawa gareta a nan gaba za ta tabbatar masa ikon da jama’a suka ba shi na mulkinsu.

Ya jaddada cewa hukuncin ba zai sa su ja da baya ba za su tsaya tsayin daka bakin ƙarfinsu domin ganin nasarar da suka samu a zaɓen ta tabbata a wannan lokaci.

Gwamman wanda ake wa laƙabi da Abba Gida-gida ya lashi takobin cewa idan har ita ma kotun ɗaukaka ƙara ba ta yi musu hukuncin da ya gamsar da su ba, za su yi amfani da damar da suke da ita wajen garzayawa har zuwa kotun ƙoli.

A yayin jawabin da ya gabatar ya kuma roƙi al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN